Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji A Sokoto Sun Kai Sumame A Maboyar Boko Haram


Wata motar sojan Najeriya ta doshi dandalin Eagle Square na Abuja, lokacin faretin cikar shekaru 150 da kafa rundunar.
Wata motar sojan Najeriya ta doshi dandalin Eagle Square na Abuja, lokacin faretin cikar shekaru 150 da kafa rundunar.

Kakakin birged ta 1, Kyaftin Yahaya Musa, yace sun kai sumame wasu wurare a Unguwar Gidan Igwai a bayan da jama'a suka tsegunta musu inda 'yan bindigar suka buya

Dakarun tsaro daga birged ta 1 ta sojojin Najeriya dake Sokoto, sun kai farmaki wasu wuraren da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram sun buya cikinsu a wata unguwar dake bifrnin Sokoto.

Sai dai ba a samu labarin mutuwa ko jikkata a wannan sumame da sojojin suka kai karshen makon nan a unguwar Gidan Igwai ba.

Mai magana da yawun birged din, Kyaftion Yahaya Musa, yace sun kama 'yan bindigar da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne a wannan sumame, amma kuma bai bayyana yawansu ba.

Kakakin yace sun kai wannan sumame ne a bayan wasu bayanai na leken asiri da kuma tallafin jama'ar gari wadanda suka ga alamun 'yan bindigar a wannan unguwa. Yace sun sanya idanu sosai kan abubuwan dake wakana a saboda fargabar cewa 'yan bindigar dake tserewa daga matakan soja a jihohin Borno da Yobe, wasunsu su na neman wuraren buya a Sokoto.

'Yan makonni kadan da suka shige ma, jami'an tsaron a Sokoto sun kai farmaki kan wata maboyar 'yan Boko Haram a birnin na Sokoto.
XS
SM
MD
LG