Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Kashe 'Yan Bindiga Biyar a Kano


Jami'an tsaro kenan ke sintiri a birnin Kano
Jami'an tsaro kenan ke sintiri a birnin Kano

Sojoji biyu sun mutu, tare da wasu tsagera su 5 a musanyar wutar da aka yi a Kano, lokacin da sojojin suka kai sumame kan wani gida da aka ce akwai 'yan tsagera ciki

a bayan da aka shafe watanni da dama ba tare da samun fitinar 'yan bindiga ba, an barke da harbe-harbe jiya asabar da asuba a birnin Kano dake arewacin Najeriya.

Jami'an soja sun ce an kashe sojoji biyu tare da 'yan bindiga biyar da ake kyautata zaton masu tsageranbcin addini ne.

Kakakin rundunar tsaro ta hadin guiwa a Kano, Kyaftin Ikedichi Iweha, ya fada cikin wata sanarwar da ya raba ta hanyar Email cewa an fara gwabzawa da misalin karfe 3 na asubahin asabar a lokacin da sojoji suka kai farmaki kan wasu gidaje guda biyu, inda aka ce akwai 'yan bindiga dake kulla makarkashiyar kai hare-hare a Kano da kuma Abuja.

An kara karfafa matakan tsaro a Kano, yayin da 'yan tawayen kungiyar Boko Haram suke sulalewa daga jihohi uku na yankin arewa maso gabashin Najeriya inda aka kafa dokar-ta-baci domin murkushe su.

A wannan sumame na jiya asabar, sojoji sun kwace bindigogi kirar AK-47 guda biyu, da daruruwan harsasai.

Kyaftin Iweha yace sun damu da ganin cewa mayakan Boko Haram su na iya hayar gidaje cikin sauki a unguwannin dake bayan garin birnin Kano. Jami'an tsaro su na shirin rushe duk gidan da aka samu dan Boko Haram a ciki tare da kama masu irin wadannan gidajen, ko da ba a cikin gidajen suke zaune ba kuwa.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun sha zargin jami'an tsaron Najeriya da laifin keta haddin jama'a, ciki har da kisa ba tare da shari'a ba, da rushewa ko lalata gine-gine da kadarori, tare da tsare mutane na har sai illa ma sha Allahu cikin mummunan yanayin da yana iya haddasa mutuwa ma.
XS
SM
MD
LG