Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bangan Fararen Hulan JTF

Dubban wadanda ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne da a ka cafke a Maiduguri mahaifar kungiyar ta'addanci mai tsatsauran ra'ayin Islama, matsan 'yan sa kai da suke kiran kansu 'Fararen Hulan JTF' suka zakulosu. 'Yan sa kan sun kwatanta kansu da sojojin JTF da aka turo su tabbatar da aiwatar da dokar ta baci da aka kakaba watanni uku da suka gabata domin farautar 'yan ta'adda. Suna cikin 'yan banga da suka taso sanadiyar aika aikar Boko Haram kungiya mai tsatsauran ra'ayin Islama wadda a ka kiyasta ta kashe mutane 1,700 a Najeriya tun shekarar 2010.

Domin Kari

XS
SM
MD
LG