Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Kashe 'Yan Boko Haram 50


Wasu sojojin Najeriya cikin mota mai sulke a Maiduguri, Jihar Borno
Wasu sojojin Najeriya cikin mota mai sulke a Maiduguri, Jihar Borno

Dakaru sun bi 'yan bindigar zuwa sansaninsu inda suka far musu ta sama da kuma ta kasa bayan da suka kashe mutane 20 a wasu kauyukan Borno

Sojojin Najeriya sun bi sawu suka kashe 'ya'yan kungiyar nan da aka fi sani da sunan Boko Haram su 50 a wani sansaninsu dake yankin arewa maso gabashin kasar.

Wani kakakin sojojin Najeriya, Kanar Sagir Musa, ya fada yau asabar cewa dakarun sun bi sawun 'yan bindigar ne a bayan da mayakan Boko Haram suka kashe mutane 20 a wasu hare-hare ranakun laraba da alhamis a wasu kauyukan Borno.

Kanar Sagir ya ce, "sojoji sun bi 'yan ta'addar zuwa cikin sansanoninsu, kuma tare da tallafin jiragen saman yaki, an kashe 'yan ta'adda guda 50 a fadan da aka gwabza."

Kungiyar Boko Haram, wadda ta yi ikirarin cewa tana so ne ta kafa tsarin shari'ar Musulunci a yankin arewacin Najeriya, da wasu kungiyoyin masu alaka da ita, sune ke haddasa barazanar tsaro mafi muni ga Najeriya, kasar da ta fi arzikin man fetur a Afirka.

Sai dai kuma al'ummar Jihar Borno da ma kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun yi zargin cewa sojoji su kan kara gishiri a irin nasarorin da suka samu tare da rage yawan dakarunsu da aka kashe ko fararen hula.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG