Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Saki Mutane 42 da Aka Tabbatar Ba 'Yan Boko Haram Ba Ne


 Babban hafsin tsaron kasa, Air Marshal Alex Badeh
Babban hafsin tsaron kasa, Air Marshal Alex Badeh

Cikin wasu mutane da sojoji suka cafke a Maiduguri da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne an saki waddanda sojojin suka tabbatar ba 'yan kungiyar ba ne

Mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar soji ta bakwai a Maiduguri Kanal Sani Usman shi ya sanar da sakin mutane 42 wadanda yace basa cikin kungiyar Boko Haram.

Yayin da mutanen suke tsare rundunar sojojin tayi masu binciken kwakwaf kuma ta tabbata ba 'yan Boko Haram ba ne. Bisa ga sakamakon binciken ya sa hukumar tsaro ta kasa ta bada umurnin sakinsu. Cikin mutanen, uku 'yan kasashen waje ne da suka hada da Chadi da Kamaru da Burkina Faso.

Sojojin basu sakesu hannu banza ba domin kowannensu an bashi nera dubu dari daya ya je ya kama wata sana'r yi. Daga bisani Kanal Sani Usman ya mikawa gwamnan Borno Kashim Shettima mutanen.

Bayan da ya karbi mutanen gwamna Shettima ya jawo hankalinsu akan bukatar su zama mutane nagari kana yayi alkawarin samar masu ayyukan yi. Ya kuma basu yadunan shadda. Yace za'a taimaka masu amma su yi imani su ji tsoron Allah idan ba haka ba kuma za'a sake kamasu.

Mutanen da aka sake sun yi matukar murna tare da godiya. Sun tabbatar cewa an taimaka masu.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG