Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Amurka Da Afghanistan Sun Yi Nadama Kan Kashe Fararen Hula


An bayyana nadama dangane da wani harin hadin gwiwa da aka kai a Arewacin Afghanistan a farko farkon watan Nuwambar bara, da ya kashe fararen hula yan kasar Afghanistan 33, da kuma raunata 27.

Ma’aikatar sojin Amurka ta bayyana haka ne yau Alhamis, a yayin fidda sakamakon bincike a kan lamarin.

Wannan mummunan harin da aka kai a kauyen Boz, da ya janyo asarar rayuka, ya lalata gidaje da dama a Lardin Kunduz a cewar mazauna yankin da kuma mayakan kungiyar Taliban.
An kai harin hadin gwiwar ne da zummar kame shugabannin Taliban dake shirin tashin hankali a yunkurinsu na kwace Lardin na Kunduz, bisa ga cewar jami’an sojin Aghanistan da kuma na Amurka.

Rundunar sojin Amurka ta bayyana yau alhamis cewa, dakarun sojan Amurka da na Afghanistan sun bude wuta a kan yan Taliban dake amfani da gidajen fararen hula suna yaki, a matakin kare kai.

An ambaci sanarwar Kwamandan rundunar sojin Amurka, Janar John Nicholson yana cewa, ko dai menene sanadi, ina matukar nadama da rashin rayukan mutanen da basu san hawa ba basu san sauka ba, yace ina tabbatarwa shugaba Ghani da mal’ummar Afghanistan cewar, zamu yi iya kokarinmu, mu tabbatar da matakan kare fararen hulan kasar.

Amurka ta bayyana bisa ga binciken da ta gudanar cewa, wadansu zaratan sojojin Afghanistan sun shirya kai farmaki a mafakar yan ta’addar Taliban Kunduztare da taimakon wani karamin rukunin sojin Amurka masu bada shawara, amma sai mayakan suka fara budewa sojojin wuta daga gidajen fararen hula da dama.

XS
SM
MD
LG