Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Za Su Ci Gaba Da Tabbatar Da Tsaron Kasa


Babban hafsan sojojin Najeriya, Janar Buratai,
Babban hafsan sojojin Najeriya, Janar Buratai,

Shugaban Aikace aikace na sojojin Najeriya Manjo Janar David Ahmadu yace sojojin kasar zasu cigaba da taka rawa wajen sha'anin tsaron cikin gida da suka ba lakani "Operation Harbin Kunama"

A yanzu dai rundunar sojoji tana ci gaba da kimtsa jami'anta bisa tanadin da kundun tsarin mulkin Najeriya ya yi domin taimaka wajen tunkarar matsalolin fashi da makami, masu garkuwa da mutane, kungiyoyin asiri da fadan kabilanci da na addini tare da kuma rikicin Makiyaya da Fulani a kudancin jihar Kaduna, inji Manjo Janar David Ahmadu.

Shirin Operation Harbin Kunama kashi na biyu zai samar da cikakkiyar nasarar fataktakar 'yan Boko Haram kwatakwata daga dajin Sambisa.

Rundunar zata yi taro da fararen hula masu ruwa da tsaki a Kafanchan jihar Kaduna da Ganawuri dake jihar Filato. Sojojin sun kuma ja hankalin mutanen Kano, Kaduna, Filato da Bauchi kada su razana lokacin da suka ga manyan mayaka suna cikin damar yaki suna kaiwa da kawowa.

Abubakar A Tsanni Mabudin Borgu daraktan wata kungiyar kishin kasa ya yabawa sojojin ya kuma nemai jama'a da su bada hadin kai domin cimma manufar tsaro.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG