Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan ta Kudu ta Sako Fursunonin Siyasa


Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir.
Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir.

​Gwamnatin Sudan ta Kudu ta bada sanarwar sako fursunoni siyasa hudu wandanda aka zarga da yunkurin juyin mulki, a wani yunkuri na farfado da hawa kan teburin shawarwari da masu adawa.

A cikin mutanen su hudu harda sakatare janar na tsuhuwar jam’iyyar Sudan People’s Liberation Movement, mai suna Pagan Mum.

Tsare wadannan mutane da akayi ya kawo cikas ga tattaunawa tsakanin gwamnatin Salva Kiir da ‘yan tawa masu goyon bayan tsohon mataimakinsa Riek Machar.

A tattaunawa da yayi da sashen turanci na Muryar Amurka, kakakin shugaban kasa Ateny Wek Ateny yace daga yanzu ‘yan tawaye baza suyi amfani da wujjar tsare wadannan mutane da ake zargi da yunkurin juyin mulki domin kin hawa teburin shawarwari.

Shine kakaki Ateny yace "wannan batu ne mai matukar muhimmanci saboda mutane hudun da ake zargi da yunkurin juyin mulki, babu wanda zai yi amfani da su yanzu a matsayin hujjar kin hawa teburin shawarwari."

Gwamnatin kasar ta kame wadannan shuwagabannin siyasa ne bayan da shugaba Kirr a watan Decembar bara ya zargi Machar da kokarin juyin mulki.

Wannan kazafi kuwa, shine yayi sanadiyar fada tsakanin sojojin masu goyon bayan Kiir, da wadanda ke goyon bayan Machar.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG