Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan Ta Musunta Amfani Da Makamai Masu Guba


Ministan shari’a a Sudan ya musunta maganar da yan gudun hijira a Jabel Marra ta yankin Darfur suka yi na cewa sun shaki iskar wani sanadari mai guba a hannun gwamnatin Sudan din.

Kungiyar rajin kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta fada jiya Alhamis cewa tun watan Janairu mutanen Jabel Marra suke bada rahoton cewa suna kamuwa da cututtuka iri-iri, kamar matsalolin fata da kaikayin jiki, har da makanta, da amai mai jni da zawayi da matsalolin numfashi.

Kungiyar Amnesty tace mutanen sun kamu da wayannan cururuta ne a sanadin makamai masu guba da hukumomin Sudan ke amfani dasu. Mutane 250 ciki har da kananan yara suka mutu, sa’annan daruruwa kuma sun samu raunuka, duk a sakamakon wannan sanadari da suke shaka.

Amma shi ministan na Shari’a na Sudan, Awad Hassan Elnour ya mayar da martini da wata wasika jiya Alhamis inda yake cewa gwamnati tayi al’ajabin jin wannan tuhuma.

Yace wannan ne karo na farko da yake jin wannan labarin wanda ke nuna kamar akwai alamar “ana aikata wani babban laifin kuntatawa wa Bil Adama” a kasar.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG