Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddama Akan Rantsarda Sabon Gwamnan Rivers


Gwamnan jihar Rivers Rotimi Amechi mai barin gado.
Gwamnan jihar Rivers Rotimi Amechi mai barin gado.

Atoni Janar na Najeriya Muhammad Bello Adoki ya umurci babban alkalin jihar Bayelsa ya rantsar da sabon gwamnan Rivers ranar 29 ga wannan watan.

Wannan umurnin na ministan shari'ar Najeriya ya haddasa cecekuce tsakanin manyan layoyin kasar.

Yakubu Saleh Bawa wani babban lauya yace abun dake faruwa a jihar Rivers wani abu sabo ne. Tunda babu babban alkali, shugaban kotunan gargajiya na jihar ya kamata ya rantsar da gwamnan amma ba wani alkali daga wata jiha ba. Yace duk alkalan Najeriya suna karkashin alkalin alkalan kasar ne. Saboda haka ministan shari'a bashi da hurumin ya ce wani alkali daga wata jiha ya rantsar da sabon gwamnan Rivers.

Shi ma Barrister Aliyu Umar wani babban lauya yace ba daidai ba ne Atoni Janar na Najeriya ya bada umurnin da ya bayar domin bashi da ikon ya dauki aikin babban alkalin Rivers ya baiwa babban alkalin Bayelsa. Ko an yi hakan za'a kalubaleshi.

A daya bangaren kuma Barrister Yakubu Saleh Bawa yace kodayake jihar bata da babban alkali shugaban kotun gargajiya ko Grand Kahdi ko alkalin daukaka kara dake jihar ka iya rantsar da sabon gwamnan jihar.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG