Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddama Tsakanin Gwamnatin Jamhuriyar Nijar Da Kungiyar Hukumar Kwastam


NIGER: Hashimi Masa'udu Ministan Tsaron Nijar
NIGER: Hashimi Masa'udu Ministan Tsaron Nijar

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta mayar da martani wa kungiyar jami’an kwastam din kasar bayan wani taron gangamin jami’an Kwastam ya nuna rashin amincewa nadin wani jami’in da ba Kwastam ba domin shugabancin hukumar saboda a cewarsu nadin ya sabawa dokar aikin Kwastam.

Batun cancantar shugabancin hukumar Kwastam a dokance shine abin da ya haddasa takon saka tsakanin gwamnatin kasar Nijar da kungiyar jami’an Kwastam na kasar, wacce tun a washegarin nadin wani babban ma’aikacin rundunar tsaron Jandarma ta bayyana rashin gamsuwa.

Kamar yadda kungiyar tace sai mutum ya shafe shekaru goma yana aiki a matsayin sufeto kafin ya cancanci wannan mukami. Sai dai Ministan Kudi ya musanta wannan magana inda yace doka bata tanadi hakan ba.

A ci gaba da kalubantar nadin Janar Ahmadou Halidou, kungiyar jami’an Kwastam tace gwamnati ta tafka kuskure domin a tarihin jamhuriyar Nijar babu gwamnatin da ta taba damka ragamar hukumar Kwastam a hannun wani wanda bai karanci wannan fanni ba.

Wannan takaddama dai na zuwa ne a lokacin da gwamnatin Nijar ta nemi hukumar Kwastam da ta matsa kaimi wajen samar mata da kudaden shiga, ta hanyar awon kaya a yayin da ‘yan kasuwa ke korafi akan hawan kudaden awo, lamarin da masana ke ganin muddin bangarorin biyu basu sasanta da juna ba zai iya kawo tarnaki wa sha’anin tattalin arzikin kasar.

Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG