Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddamar Filaye Tsakanin Rundunar Sojojin Najeriya Da Yan Asalin Abuja


Wasu ‘yan asalin Abuja daga gundumar Tunga Maje sun gudanar da wata zanga zangar lumana, inda sukayi korafin cewa rundunar sojan Najeriya na son mamaye musu filaye.

Zanga zangar dai ta kai ga hedikwatar ma’aikatar shari’a ta Najeriya da majalisar Dattawan Najeriya da kuma ofishin Ministan Abuja. A cewar Alhaji Jibrin Mamman, tun asalin iyaye da kakanni suke zaune a wannnan yanki, amma yanzu sojoji sun basu wa’adin ranar 1 ga watan Disambar wannan shekara da su kwashe nasu ya nasu su bar filayen, idan ba haka ba zasu kore su.

Kan wannan korafi ne wakilin Muryar Amurka, Hassan Maina Kaina, ya tuntubi shugaban sashen kula da kaddarorin hedikwatar sojan Najeriya, Manjo Janar PAT Akem, wanda yace “rundunar sojan Najeriya bata mamaye filayen al’umma, muna amfani ne da filayen da hukuma ta bamu a hukumance kuma gwamnati na bamu fili ko a Jaji, Zariya, Kano, Akwa Ibom ko Lagos, don mu assasa cibiyoyinmu na soja idan har mutanen Zariya ko Jaji zasu sadaukar da filayensu don kishin kasa wata rana a wayi gari suce suma a basu filayensu, kaga kenan wata rana za a wayi gari babu sojojin da zasu kare muradun kasa. Mu bama mamaye filaye dukkan filin da muke da su gwamnati ce ta bamu.”

Kasancewar ma’aikatar raya birnin tarayyar Abuja, itace ke da alhakin raba filaye a birnin Tarayyar muka tuntubi kakakin ministan birnin Mallam Abubakar Sani, wanda yace duk lokacin da aka samu irin wannan rashin fahimta tsakanin jama’a, a rubuta zuwa ga Ministan Abuja domin a dauki mataki akai.

Yanzu abin jira a gani shine yadda za a warware wannan takaddamar tsakanin ‘yan asalin Abuja da kuma rundunar sojojin Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

XS
SM
MD
LG