Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarayyar Turai ba zata bari 'yan gudun hijira su nemi dawowa daga Turkiya ba


Ana jigilar 'yan gudun hijira daga Girka zuwa Turkiya
Ana jigilar 'yan gudun hijira daga Girka zuwa Turkiya

A daidai wannan lokaci da kasar Turkiyya ke shirin karbar ‘yan gudun hijira rukuni na biyu, kungiyar tarayyar Turai a jiya Laraba tace, ba wasu ‘yan gudun hijirar da zasu sami wata damar dawowar ganin dama bat un kafin su sami damar neman takardun neman mafaka ba.

Wannan sanarwa ta biyo bayan zanga-zangar wasu ‘yan rajin kare hakkin bil’adama dake adawa da tsarin wanda suka zargi Turan da danne hakkin ‘yan gudun hijirar na neman mafaka tun kafin ace an fara kwashe su daga Lesbos da Chios.

Kakakin ofishin tallafin neman mafaka na Tarayyar Turai Jean-Pierre Schembri ya fadawa Muryar Amurka cewa, ba wata bada damar sake dawowa ta kai tsaye ga ‘yan gudun hijirar, amma za’a bawa kowannensu dama in har suna neman mafakar a hukumance.

Schembri dai na cikin jami’an Turai guda 70 da suka isa tsibirin a jiya Laraba, don lura da ayyukan neman mafakar ‘yan gudun hijirar a hukumance, bayan wannan zanga zangar adawa da kwashe bakin, biyo bayan yarjejeniyar watan Maris tsakanin Turkiyya da Tarayyar Turai don magance matsalkar kwararar ‘yan gudun hijira.

XS
SM
MD
LG