Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Kasa Ya Amince da Mutane Hamsin Mafiya Hikima


Majalisar Najeriya
Majalisar Najeriya

Taron kasa da ake gudanarwa a Abuja, ya amince da mutane hamsin mafiya hikima don shata yanda za’a kada kuri’ar amincewa da kudurorin taron.

Yanzu haka dai kashi saba'in cikin dari ne na kuri'a ake bukata kuma hakan zai zama da faida ga ‘yan arewa dake ganin basu da rijaye a taron.

Batun da yafi daukan hankali shine na dagewa domin bin ka'idojin taraiyya inda larduna ko jihohi zasu raba ikon arzikin yankunansu, da wasu dokokin su, yayin da gwamnatin taraiyya zata zama mahada ko kuma lemar gamayya.

Ita kuma da take jawabi a wujen taron, Farfesa Gambo Laraba Abdullahi cewa tayi man fetur na hana mu fadada hanyoyin bunkasa tattallin arzikin Najeriya.

Farfesa Gambo tace "
Taron Kasa akan Taraiya - 3'15"
XS
SM
MD
LG