Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tasirin Darajar Naira a Harkokin Kasuwancin Kasar Nijar


Women dance wearing lights during the lantern festival, part of the Chinese New Year celebrations, on the waterfront in Wellington, New Zealand.
Women dance wearing lights during the lantern festival, part of the Chinese New Year celebrations, on the waterfront in Wellington, New Zealand.

A Jamhuriyar Nijar 'yan kasuwa na kokawa da darajar Naira saboda farashin kayan da suke sawowa daga Najeriya basu canza ba duk da fadi tashin dalar Amurka a cudanyarta da Naira

Inji Ibrahim Mai Shayi yace saboda darajar Naira dake karuwa ana iya sayen kaya yau a Illelan Najeriya gobe a koma watakila dalar Amurka ta fadi, Naira ta kara daraja.

Yace kayan da aka saya yanzu an juma kadan farashin na iya sauyawa bisa ga darajar Naira saboda ba wuya a kara kudi domin wai Naira ta kara daraja. Ga masu zuwa Najaeriya daga Jamhuriyar Nijar lamarin ya rincabe masu.

A kasuwar kasa da kasa dake Illela a jihar Sokoto mai tazarar kilomita biyar kacal da birnin Konni a Jamhuriyar Nijar inda 'yan kasuwa daga sassan Najeriya da na Nijar ke halarta a kowane mako sun ce duk da farfadowar Naira sha'anin kasuwanci bai canza zani ba.

Kazalika sun kara tsunduma wajen tsadar kaya daga tarayyar Najeriya. Malam Isa yace basa jin faduwar Naira saboda kaya sun kara tsada kuma dole su kara ma nasu kayan kudi a cikin Nijar. Yin hakan kuma ya kansa mutanen gari su ga tsadar kayan.

A Najeriya darajar Naira ta tashi amma kuma 'yan kasuwan kasar basu rage farashin kayansu ba.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG