Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawaga da ta hada da wakilan Majalisar Dinkin Duniya na ziyarar arewa maso gabashin Najeriya


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon

Wata tawaga da ta hada da wakilan majalisar dinkin duniya da bankin duniya da tarayyar turai na ziyarar arewa maso gabashin Najeriya ta gani da ido irin barnar da kungiyar Boko Haram ta haddasa da zummar taimakawa da farfado tattalin arzikin yankin

Alhaji Wakili Adamu na ofishin mataimakin shugaban kasar Najeriya ya jagoranci tawagar wadda ta fara yada zango a Bauchi.

Kokarin gwamnatin tarayya da na jihohin da rikicin Boko Haram ya shafa ya sa Majalisar Dinkin Duniya da Bankin Duniya da Tarayyar Turai suka hada tawagar gani da ido irin halin da jihohin da Boko Haram ta daidaita ke ciki.

Manufar ziyarar itace ta tara bayanai kan irin barnar da kungiyar Boko Haram ya yi a yankin. Bisa ga rahoton ne ita MDD da Bankin Duniya da Tarayyar Turai zasu bada tallafin da zai farfado da tattalin arzikin yankin. Akwai jihohi shida a yankin.

Umar Musa Shehu shugaban 'yan gudun hijira a arewa maso gabas yana cikin tawagar ya kuma bayyana aniyarsu na ganin duk 'yan gudun hijira sun koma gidajensu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG