Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Gwamnatin Kano Ta Ziyarci Makarantar Hadin Gwuiwa Tsakaninta da Nijar dake Yamai


Gwamnan Jihar Kano Dr Ganduje da gwamnatinsa ta aika da tawaga zuwa makarantar hadin gwuiwa da gwamnatin Nijar dake Yamai
Gwamnan Jihar Kano Dr Ganduje da gwamnatinsa ta aika da tawaga zuwa makarantar hadin gwuiwa da gwamnatin Nijar dake Yamai

Kimanin dalibai 548 maza zalla daga jihar Kano da jihohin Nijar ke daukan karatu a makarantar hadin gwuiwa tsakanin gwamnatin Kano da Nijar da aka kafa a Yamai

An bude makarantar ta hadin gwuiwa ne domin yaran Kano da Nijar su koyi harsunan turanci da faransanci a wata hanyar kara cudanya tsakanin kasashen biyu.

Mataimakin gwamnan Kano Farfasa Hafis Abubakar shi ya jagoranci wata tawaga daga Kano domin ziyartar kwalajin. Ya bayyana gamsuwa da yadda ya tarad da daliban. Yace sun zo su duba, su ga yanayin da makarantar take.

Farfsa Abubakar yace sun ga yaran suna cikin koshin lafiya kuma suna koyon karatu sosai.

Mako guda kafin zuwan tawagar daliban sun yi korafi akan wasu matsaloli ciki kuwa har da cunkoson dalibai a dakunan kwana sakamakon rashin wadatar katifu. Da aka tambayi Farfasa Abubakar akan lamarin yace akwai katifu suna nan a hannu kwastan domin an taho dasu daga Kano amma aka samu dan tsaiko. Yace gwamnati ta shiga cikin lamarin ta dauki mataki.

Minista ilimin sakandare na kasar Nijar Alhaji Sani Abdulrahaman ya tabbatarwa daliban cewa gwamnatin Nijar ba zata yi kasa a gwuiwa ba wajen bunkasa harkokin koyaswa a makarantar wadda ke shirin yaye dalibanta na farko a karshen shekarar karatun bana.

Wakilin dalibai dalibi daga jihar Kano Tsalha Musa ya godewa hukumomin Najeriya da Nijar akan dabarar bude makarantar.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG