Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Ministan harkokin cikin gida na Najeriya ta ziyarci jihar Borno


Ministan Harkokin Cikin Gida na Najeriya Janar Abdulrahaman Bello Dambazau
Ministan Harkokin Cikin Gida na Najeriya Janar Abdulrahaman Bello Dambazau

Tawagar ministan harkokin cikin gidan Najeriya da ta hada da babban sifeton 'yansanda da manyan daraktocin gidan yari da shige da fici da wasu ma na ziyarar gani da ido a jihar Borno.

Janar Dambazau da babban sifeton 'yansanda Solomon Arase da kwantrolan hukumar shige da fice da na gidan yari da na 'yansandan fararen kaya da ma wasu sun kai ziyarar gani da ido zuwa jihar Borno.

Tawagar na Borno ne domin duba lamuran da suka jibanci harkokin tsaro. Sun fara da fadar gwamnatin jihar kafin su gana da Shehun Borno Alhaji Abubakar Umar ibn Garbai El-Kanemi.

Tawagar ta ziyarci sansanin 'yan gudun hijira dake Dalori wanda yake da ya kasance mafi yawan jama'a.Yana da 'yan gudun hijira fiye da 15,000 da suka hada da mata da kuma kananan yara.

Ministan Janar Dambazau ya yiwa 'yan gudun hijiran jawabi. Ya yabawa sojojin yakin sama da suka samar ma sansanin wajen kiwon lafiya da kuma daidaikun jama'a da suka bada tasu gudummawa.Yace zasu yi iyakar kokarinsu su ga mutanen sun koma garuruwansu cikin dan lokaci. Duk garuruwan da aka kwato za'a sa masu jami'an tsaro domin kada 'yan ta'ada su sake farmasu.

Da tawagar ta wuce jihar Yobe sai gwamnan Borno ya rabawa 'yan sakai ko kato da gora motoci da yi masu alkawarin daukan dawainiyar kudin asibitocinsu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:41 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG