Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Yace Nasarar Da Ya Samu Gagaruma Ce


Donald Trump bukaci hadin kan 'ya'yan jam’iyyar Republican

Shugaban jam’iyyar Republican na Amurka yace yana ganin cewa yanzu ta tabatta da cewa kusan Donald Trump ne wanda jam’iyyar zata tsaida a matsayin dan takarar shugaban kasa bayan da ya sami nasara a zaben fidda gwanin da aka yi jiya a jihar Indiana.

Trump ya sami kuri’u kashi 53 cikin dari, Sanata Ted Cruz kuma ya zo na biyu da kashi 37, da ga nan sai gwamnan jihar Ohio John Kasich, wanda ya sami kashi 7 cikin dari na kuri'un da aka jefa.

Bayan kayen da ya sha a zaben da aka yi jiya a jihar Indiana a kokarin da ya ke yi don ganin ya takawa Trump burki wajen samun wakilan da jam’iyyar Republican ke bukata don fidda dan takara, Cruz ya janye daga takarar. Ya fadawa magoya bayansa cewa babu damar ya cigaba da gwagwarmayar neman takara tunda masu zabe sun zabi wani.

Trump ya ce nasarar da ya samu gagaruma ce. Ya kuma yabawa Cruz, yana mai cewa Cruz din da sauran wadan da suka kara da shi sunyi kokari. Trump kuma yai kiran hadin kan jam’iyya.

Shima shugaban jam'iyyar ta republican, Reince Preibus, irin sakon da ya aikawa 'yan jam'iyyar ke nan, inda ya neme su hada kai don samun galaba akan Hilary Clinton.

A jam’iyyar Democrat kuma, Sanata Bernie Sanders ya doke abokiyar takararsa Hilary Clinton a zaben na jihar Indiana, inda ya sami kashi 53 cikin dari na kuri'un da aka jefa jiya. Amma duk da nasarar da ya samu a jiyan, har yanzu akwai tazara sosai tsakanisa da Clinton, yana neman gagarumar nasara a zaben da za a yi a sauran jihohin da suka rage kafin ya iya sha gabanta.

XS
SM
MD
LG