Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Yace Amurka Ta Hana Musulmi Shigowa Kasar Sai Tayi Tantancewa


Donald Trump dan takarar shugaban kasar Amurka a karkashin jam'iyyar Republican
Donald Trump dan takarar shugaban kasar Amurka a karkashin jam'iyyar Republican

Dan takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyyar Republican Donald Trump yayi kira ga Amurka "baki daya ta hana duk wani musulmi shigowa kasar, har sai shugabannin kasar sun "tantance abunda ke faruwa."

Trump yace sakamakon kuri'ar neman jin ra'ayin jama'a ya nuna "Musulmi masu yawa suna da matukar kiyayya," ga Amurkawa.

"Har sai mun gano kuma muka fahimci wannan matsala, da kuma irin hadari da barazanar da zasu haddasa, kasar mu ba zata ci gaba da fuskantar hare hare daga mutanen da babu abunda suka amanna da shi illa jihadi, kuma basu da tunani ko tsinkaya da kuma mutunta ran Bil'Adama.

Bakar magana kan musulmi ba wani sabon abu bane ga Donald Trump, wanda yayi kira ga gwamnati ta saka ido kan masallatai, kuma bai debe shawararsa ta farko na saka sunayen musulmi dake Amurka cikin wani kundi na musamman ba.

Kalaman na Mr. Trump sun zo ne kwana daya bayan da shugaban Amurka Barack Obama yayi kira ga Amurkawa kada suna kyama ga musulmi, lokacinda yake jawabi kan harin ta'addancin da aka kai garin San Bernadino a California.

Fadar White ta shugaban Amurka bata yi wata wata ba wajen yin Allah wadai da shwarar da Trump ya bayar, tana cewa "baki daya shawarar ta saba halayya da tunanin Amurkawa.

Republican presidential candidate Donald Trump speaks during a campaign rally, Dec. 5, 2015, in Davenport, Iowa.
Republican presidential candidate Donald Trump speaks during a campaign rally, Dec. 5, 2015, in Davenport, Iowa.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG