Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CIA-Zan Baku Cikakken Goyon Baya-Trump.


Trump a hukumar leken asiri ta CIA ranar Asabar.
Trump a hukumar leken asiri ta CIA ranar Asabar.

Trump ya bayyana haka a gaban ma'aikatan hukumar su 400 a helkwatar CIA a Virginia.

Shugaban Amurka Donald Trump, ya gayawa ma'aikatan hukumar leken asiri ta Amurka CIA cewa su kwan-da- sanin "yana basu cikakken goyon baya."

Mr.Trump ya bayyana hakan ne jiya Asabar, lokacinda ya kai ziyara a helkwatar hukumar dake unguwar Langley a jahar Virginia, a cikakkiyar ranar da yayi aiki a zaman shugaban Amurka.

"Na sani wani lokaci, ba kwa samun cikakken goyon bayann da kuke bukata, amma yanzu zaku sama matukar goyon baya. Watakil har kuce, don Allah ya isa haka," inji sabon shugaban na Amurka, furucin da ya sa ma'aikatan suka fashe da dariya.

Jami'an hukumar ta CIA suka ce kimanin ma'aikatan hukumar 400 n suka halarci taro da shugaba Trump.

Mr.Trump ya fito fili ya bayyana cewa yaki da kungiyar ISIS, shine babba akan ajendar gwamnatinsa, kuma yace gwamnatinsa zata karfafa matakan da take dauka.

Ana kallon ziyarar a zaman wani yunkuri na inganta dangantaka tsakaninsa da ma'aikatan hukumomin leken asirin Amurka, wadanda Mr. Trump ya ja daga da su, musamman a baya bayan nan kan bayanai da suka nuna cewa kasar Rasha ta yi shishshigi ga zaben Amurka, da nufin taimakawa Mr. Trump ya sami nasara.

Jami'an aikin leken asiri suka ce kalaman Trump na kaskantarda aikinsu yayi illa ga kwarin guiwar ma'aikata.

Wani tsohon ma'aikacin hukumar ta fuskar yaki da ta'adanci Aki Peritz, yace ma'aikatan na CIA masu basira ne, kwararru, kuma masu ilmi. "jawabi daya irin wannan ba zai sa su sauya ra'ayinsu kan damuwar da suke da ita dangane da sabon shugaban na Amurka ba.

A jawabin nasa Mr.Trump yace dalilin ziyararsa shine domin ya dade yana sa in sa da 'yan jarida, wadanda yace suka sa ana kallo kamar yana da damuwa da hukumomin leken asiri.

Ziyarar da Mr. Trump ya kai hukumar CIA tana zuwa ne bayan da 'yan jam'iyyar Democrat a Mjalaisar dattijai suka sami nasarar jinkirta tantance sabon shugaban hukumar dan majalisar wakilai Mike Pampeo zuwa Litinin.

Haka nan a wuni na biyu na shugabancinsa Trump da iyalansa da mataimakin shugaba kasa Mike Pence, sun halarci addu'o'i a babban zauren ibada ta kasa dake nan birnin Washington.

Haka nan Mr.Trump yayi amfani da shafinsa na Twitter wajen yin godiya ga Amurkawa saboda sun fito domin bikin kama aikinsa. Haka nan ya godewa kafofin yada labarai saboda jinjinawa jawabinsa na kama aiki.

XS
SM
MD
LG