Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsageru Sun Kai Hari Kamfanin Chevron a Nigeria


kamfanin man fetur da aka kai ma hari
kamfanin man fetur da aka kai ma hari

Rundunar sojojin ruwan Najeriya ko Navy ta sanar jiyar Alhamis cewa wasu mayakan sa kai sun farma kamfanin hakan man fetur na Chevron a matsayin wani hari na baya bayan nan da suka aiwatar a yankin Niger Delta

Harin ya sa an fara fargaban komawa irin hare-haren da aka saba yi a yankin na Niger Delta.

Yankin yayi kamarin suna lokacin da 'yan mayakan sa kai daga al'ummoni yankin suka fara neman a basu kaso mai tsoka cikin dukiyar man fetur da Najeriya ke samu. Basu daina kai hare-hare ba sai da gwamnatin tarayya ta soma biyansu a shekarar 2009.

Mai magana da yawun Navy Chris Ezekobe ya fadawa Muryar Amurka mayakan sun yi anfani da nakiyoyi ne suka fasa tankunan da ake tara man fetur da iskar gas dake kusa da wata tashar jirgin ruwa ta Escravos a jihar Niger Delta. Lamarin ya fara faruwa ne ranar Laraba da yammaci.

Ezekobe yace babu wanda ya rasa ransa saidai bai sani ba ko mai ya bata filayen wurin.

Yace kodayake ba'a rufe kamfanin Chevron din ba gaba daya amma baya iya fitar da mai kamar da saboda barnar da mayakan suka yi.

A cikin wani fili a yanar gizo wata kungiya dake kiran kanta kungiyar daukan fansa ko Niger Delta Avengers ta dauki alhakin kai harin. A can baya kungiyar ta sha daukan alhakin kai hare hare akan bututan mai a yankin na Niger Delta.

Kodayake yankin na Niger Delta ke samar ma Najeriya yawancin arzikinta amma har yanzu yana cikin talauci da rashin abun more rayuwa. Dalili ke nan da ake samun yawan aikata manyan laifuka da sace mutane da sace sace da kai ma kamfanonin hakan mai hari.

Watan da ya gabata Shugaba Muhammad Buhari ya lashi takobin jima masu kai hari kan kamfanonin hakan mai kamar yadda yake yi da 'yan ta'adan Boko Haram, kungiyar da ta kwashe shekaru da dama tana yaki da sojoji tare da hana al'ummomin arewa maso gabashin Najeriya sakat.

XS
SM
MD
LG