Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsagerun Matasan Nigeria Dauke da Makamai Sun Kai Hari Kusa da Birnin Maiduguri


Sojoji da 'yansanda sun shiga sintiri bayan harin da ake zato 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai kusa da sansanin mayakan sama a Maiduguri ranar 2 ga watan Disamba shekarar 2013.
Sojoji da 'yansanda sun shiga sintiri bayan harin da ake zato 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai kusa da sansanin mayakan sama a Maiduguri ranar 2 ga watan Disamba shekarar 2013.

An kaiwa cibiyar Jihar Borno hare-hare masu karfi a karon farko tun kafa dokar ta baci a watan Mayu

Rundunar sojin Nigeria, ta bada rahoton cewa ‘yan tsagerar da ake kyautata cewar ‘yan Boko haram ne sun kai hare-hare cibiyoyin soja da na ‘yan sanda dake wajen birnin Maiduguri da safiyar Litinin- harin da ake kyautata cewar shine irinsa na farko mafi muni da aka kaiwa babban birnin jihar Borno tun kafa dokar ta bacin da aka yi a watan mayun da ya gabata. Ba’a ji ta bakin jami’an hukuma ba game da yawan wadanda suka jikkata ko rasa rayukansu daga dukkan sassa biyun ba.

Sai dai hare-haren sun barnata hanyoyi masu tazarar kilomita masu yawa a tsakanin sansanin sojin jiragen saman Nigeria da kuma barikin bataliyar rundunar soja ta 33. Anga matasa da kananan yara sun yi cincirindo a kewaye da konannun gawarwakin wadaanda ake zargin ta masu kai hare-haren ne a kan kekuna.Sannan wanda yaga abinda ya faru da idonsa ya nuna gawa da yatsansa yana cewa kunga Dan Boko haram ne dake dauke da bindiga a hannunsa- hadin gwiwar soja da mutanen gari suka kama sannan suka harbe shi, amma suka kawo gawarsa nan suke jefar amma suka cinna wuta a gawar domin konata.

Wani abin mamakin shine yadda mutane ke taruwa suna kallon yadda ake konar gawar. Gefe daya kuma mazauna inda ake konar gawar suka rika nunawa da yatsunsu konanniyar motar da duk jikinta tabon harbe-haren bindigogi ne. ‘Yan kallon kuma suka rika nunawa ‘yan jarida gawarwakin mazauna wurin biyu da suka ce harbesu aka yi suka mutu har lahira, kuma an harbesu ne a kansu.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG