Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsaurin Ra’ayi: Kungiyar Dalibai Musulmi Ta Ce Za Ta Sa Ido


Wasu matasa na tattauna hanyoyin cigaba
Wasu matasa na tattauna hanyoyin cigaba

Ana cigaba da samun kungiyoyi masu ba da gudunmowa a kokarin da ake wajen kare matasa daga masu cusa masu tsauraran ra'ayoyi

Kungiyar dalibai Musulmi a Najeriya (MSS a takaice) ta ce za ta shiga yaki da da tsattsauran ra’ayi gadan-gadan ta wajen sa ido kan dalibai Musulmi ‘yan Najeriya da ke kasashen waje – musamman wadanda ke kasashen larabawa. Ta ce daukar wannan matakin ya zama dole ganin yadda ake ta cusa ma daliban tsauraran ra’ayoyi yayin da su ke dalibta a irin wadannan kasashen.

Shugaban kungiyar na Najeriya baki daya, Alhaji Muhammad Jameel Muhammad, ya fada a wani taron kaddamar da shirin koyar da sana’o’i da ilimin zamantakewa da kungiyar ta shirya a Minna, fadar gwanatin jahar Naija, cewa tuni ma kungiyar ta shiga hada gwiwa da wasu takwarorinta na kasashen waje.

Malam Jameel y ace a shekarar da ake gab da shiga za a yi wani gawurtaccen taron kungiyoyin Musulmi na Afirka baki daya a garin Sakkwaton Najeriya, inda za a kara jaddada hakan kamar yadda aka yi a baya. Y ace har Amurka ma za su je don ganawa da sauran Musulmi dalibai.

Ga wakilinmu a Minna Mustafa Nasiru Batsari da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG