Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Tsohon Gwamnan Bauchi Zai Mayar Da Naira Biliyan 80.’ - APC


Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda
Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda

Batun binciken jami'an gwamnatin Bauchi da ta shude ya shiga wani sabon mataki ta yadda kwamitin binciken ya shawarci gwamnatin Bauchi ta APC da ta sa tsohon gwamna Isa Yuguda ya amayo Naira biliyan 80

Gwamanatin APC mai mulki a jihar Bauchi ta zargi gwamatin da ta shude na PDP karkashin mulkin Malam Isa Yuguda da dulmiyar da kudaden gwamnatin jahar fiye da naira miliyan dubu dari da tamanin a tsawon shekaru takwas da ta yi mulki a jihar Bauchin.

Shugaban kwamitin karbo kayayyakin gwamnatin jihar Bauchin da aka dauka ba bisa ka’ida ba Air komodo mai ritaya Ahmed Tijjani Baba Gamawa ya bayyana hakan a rahoton kwamitin da ya gabatar wa gwanan Bauchin Barrister Ahmed Abdullahi Abubakar.

Amma kakakin tsohuwar gwamantin Malam Isa ya ce babu sisin kwabon da aka kashe ba tare da samun izini ba; hasali ma kwamitin bai gayyaci wani jami’in tsohuwar gwamnatin domin jin ba’asi ba.

Ga wakilinmu Abdulwahab Muhammad da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00
Shiga Kai Tsaye


Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG