Kafara yada labaran kasar ta Turkiyayy a yau Juma’a ta ruwaito cewa an samu Muwafaka Alabash da Asem Alfrhad da laifin fasa kwaurin mutane.
Daga cikin ‘yan gudun hijrar da suka mutu, akwai Aylan Kurdi mai shekaru uku, wanda mutuwarsa ta ja hankalin duniya tare da nuna irin matsanancin halin da ‘yan gudun hijra ke ciki.
An tsinci gawarsa ne a gabar teku kasar ta Turkiyya, sannan mahaifiyarsa da mahaifinsa ma sun rasa rayukansu.
A ranar 11 ga watan Fabrairu aka fara sauraren shari’ar a wata kuto da ke yammacin garin Bodrum.
Iyayen Aylan Kurdi na daga cikin dubun dubatan ‘yan gudun hijra da suka saida ransu suka bi ta teku domin kaiwa ga kasar Turkiyya, da zimmar rayuwa mai inganci a kasashen arewacin da yammacin nahiyar Turai.
Kididdiga ta nuna cewa akalla masu neman mafaka miliyan 1.25 ne suka isa nahiyar turai tun daga shekarar 2015, adadin da ya ninka wanda aka gani a shekarar 2014.