Accessibility links

Uganda: Gwamnati ta damke tsohon babban jami'in leken asiri


Janar David Sejusa mi adawa da mulkin shugaban Uganda da agwamnati ta damke

Janar David Sejusa mi adawa da mulkin shugaban Uganda da agwamnati ta damke

Gwamnatin Uganda, ta ce jiya Lahadi a birnin Kampala ne dakarun tsaron kasar suka damke tsohon babban jami’in leken asiri na kasar, Janar David Sejusa, wanda ya bayyana shugaba Yoweri Museveni a zaman dan mulkin kama karya.

Sojoji sun shafe awa biyu da rabi sun a binciken gidansa kafin su kama shi.

Wannan yana zuwa ne a yayin da kasar Uganda take shirin gudanar da zaben shugaban kasa ranar 18 ga wannan wata, inda shugaba Museveni, wanda yah au mulki tun shekarar 1986, yake neman a sake zabensa.

Kakakin gwamnatin Uganda, Ofwono Opondo, yace an kama Janar Sejusa a saboda yana tsoma hannunsa a cikin harkokin siyasa.

Opondo yace Janar Sejusa yana jawabai a bainar jama’a yana barazanar harhada kawunan jama’a su kauracewa zaben wanda a cewarsa na bagu ne kawai.

Lauyan Sejusa, Ladislaus Rwakafuzi, ya fadawa VOA cewa kama janar din da aka yi haramun ne a saboda sojoji basu da takardar iznin kama shi, kuma sun ki bayanin dalilansu na yin hakan.

Lauyan yace watakila kama Janar din yana da alaka da zabe mai zuwa a saboda yana bayarda shawara ga babban shugaban adawa na kasar, Kizza Besigye, kan yadda za a iya hana magudi a lokacin zabe.

XS
SM
MD
LG