Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Uganda: 'Yansanda sun tsare shugaban hamayyar siyasar kasar


Shugaban hamayya Kizza Besigye cikin farar riga da 'yan sanda suka kama
Shugaban hamayya Kizza Besigye cikin farar riga da 'yan sanda suka kama

‘Yan sanda sun tsare shugaban ‘yan adawa na kasar Uganda, Kizza Besigye, na wani dan lokaci kafin su sako shi yau litinin, a yayin da yake kyamfe na zaben shugaban kasar da za a gudanar cikin wannan makon.

Shaidu sun ce ‘yan sanda sun harba barkonon tsohuwa kan wani taron laccar siyasa ta Besigye a Kampala, babban birnin kasar, suka kuma kama shi. Daga nan suka dauke shi zuwa wani wuri a wajen birnin na Kampala kafin su sake shi.

An sha kama Besigye ana kullewa cikin ‘yan shekarun nan a yayin da yake jagorancin zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin shugaba Yoweri Museveni.

A ranar alhamis ‘yan kasar Uganda zasu je su rumfunan zabe domin kada kuri’unsu ma shugaban kasa da ‘yan majalisun dokoki na kasa da na yankuna.

Museveni yah au kan kujerar shugabancin Uganda tun wani juyin mulki a shekarar 1986, sannan ya lashe zabubbuka a 2006 da 2011 da gagarumin rinjaye. ‘Yan kallo sun bayyana zabubbukan a zaman na magudi, inda aka yi ta tursasawa jam’iyyun adawa.

Wannan shi ne karo na hudu da Besigye yake takarar shugabancin Uganda.

XS
SM
MD
LG