Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Umaru Musa 'Yar'aduwa Ya Rasu


Umaru Musa 'Yar'aduwa
Umaru Musa 'Yar'aduwa

Shugaba Barack Obama na Amurka ya bayyana jimamin rasuwar 'Yar'aduwa yana mai bayyana shi a zaman kamilin mutum.

Gwamnatin Najeriya ta bayar da sanarwar rasuwar shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa, wanda ya jima yana fama da rashin lafiya.

Wata sanarwa a gidan rediyon kasar ta ce marigayin ya rasu laraba da maraice a cikin fadar shugaban kasa. Ya rasu yana da shekaru 58 da haihuwa.

Ba a bayar da sanarwar sanadiyyar rasuwar ta sa ba.

Tun a karshen watan Nuwamba shugaba 'Yar'aduwa yake kwance yana jinya, ya kuma shafe watanni uku yana kwance a asibiti a kasar Sa'udiyya a sanadin kumburin rigar zuciya.

Rashin kasancewarsa a Najeriya ta jefa kasar cikin rikicin siyasa wadda har ta kai ga rantsar da mataimakinsa, Goodluck Jonathan, a matsayin shugaban riko a watan Fabrairu.

Marigayi Shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa
Marigayi Shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa

'Yar'aduwa ya koma Najeriya a watan Fabrairu, amma tun lokacin ba a gan shi a bainar jama'a ba.

Da asubahin yau alhamis fadar shugaban Najeriya ta bayar da sanarwar zaman makoki na kwanaki 7, ta kuma ce za a binne marigayin bayan azahar a Katsina. Wani kakakin shugaban yace mai dakinsa, Turai 'Yar'aduwa, tana kusa da shi a lokacin da ajalinsa ya cika.

A nan Washington, shugaba Barack Obama na Amurka ya bayyana bakin cikin rasuwar 'Yar'aduwa, yana mai bayyana shi a zaman kamilin mutum, kuma mai gaskiya. Shugaban na Amurka ya yaba ma 'Yar'aduwa a zaman mutum wanda yayi imani sosai kan makomar kasarsa.

Shugaba 'Yar'aduwa ya jima yana fama da rashin lafiya. A bayan wannan ciwo na zuciya da ya kwantar da shi kwanakin baya, an san cewa yana fama da ciwon koda.

An bayyana rasuwarsa a zaman wadda za ta haddasa rarrabuwar kawuna a jam'iyyar PDP mai mulkin kasar. Mai rikon mukamin shugaba Goodluck Jonathan bai fito yace ba zai yi takarar wannan kujera a shekara mai zuwa ba.

Amma kuma ya fito ne daga kudancin Najeriya. Shugaban jam'iyyar ta PDP yace ya kamata dan takarar shugaban kasa na gaba ya fito daga arewacin Najeriya domin kammala wa'adin shekaru 8 da aka yi ma 'yan siyasar arewa a karkashin wani tsari na jam'iyyar na yin karba-karba a tsakanin arewaci da kudancin Najeriya.

XS
SM
MD
LG