Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Vladimir Putin Ya Amince Wajan Dawo Da Cikakkiyar Dangantaka Da Turkiyya


Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya amince da yin aikin da zai dawo da cikakkiyar dangantakar sa da kasar Turkiyya, amma yace dawo da harkokin cinikayya tsakanin kasashen biyu zai ‘dauki lokaci.

A jiya Talata ne bayan da shugaban kasar Rasha Puttin ya gana da takwaransa na Turkiyya Tayyip Erdogan a birnin Saint Petersburg na Rasha, yace “a kokarin dawo da mu’amula ta hanyar cinikayya da tattalin arziki, yanzu haka an fara ta, amma zai ‘dauki lokaci.”

Erdogan yace kasashen biyu zasu dawo da yarjejeniyar cinikayyar da ke tsakaninsu da ta kai Dala Biliyan 100, kuma za a gaggauta dawo wa da ita.

Shugaban na Turkiyya ya kara da cewa, a shirye yake ya gina bututun iskar gas da kasar Rasha, kuma zai tattauna da Rasha don ganin Turkiyya ta gina wajen sarrafa makamashin Nukiliya na farko a kasar.

Kasashen biyu dai sun amince da sake wani zama domin samun hanyar da za a kawo karshen yakin da ake A Siriya. Baki daya kasashen biyu na goyon bangare daban daban a yakin basasar Siriya.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG