Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wadanda Suka Kai Hari a California Sun Dade da Baudewa - FBI


Mutane 14 da maharan suka kashe a jihar California
Mutane 14 da maharan suka kashe a jihar California

Hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka FBI tace hukumomi sun hakikance cewa mata da miji Syed Farouk da Tashfeen Malik wadanda ake zargi da kai hari a garin San Bernadino dake jihar California makon jiya, "sun juma da baudewa,"kuma akwai shaidar sun kitsa kai wannan mummunar hari.

David Bowdich shine mataimakin darektan FBI mai kula da shiyyarta dake Los Angeles ya gayawa manema labarai jiya Litinin cewa,maharan sunyi gwajin harbe harbe na ‘yan kwanaki kamin su kai harin na makon jiya. Yace har yanzu hukumar ta FBI tana binciken tsawon lokacin da maharan suka dauka suna shirya kai wannan hari. Duk da haka yace zuwa yanzu dai babu shaidar cewa wadannan mutane 'yan wata kungiya ce ko suna karbar umarni daga ketare.

Ahalinda ake ciki kuma, biyo bayan harin na makon jiya, hukumar tsaron-gida ta Amurka ta bada sanarwar jiya Litinin cewa zata bullo da wani sabon shiri na fadakarwa ko ankarar da Amurkawa kan yiyuwar ana shirin kawo harin ta'addanci a nan Amurka.

Wadanda suka kai harin Tashfeen Malik da mijinta Syed Farouk

APTOPIX California Shootings
APTOPIX California Shootings

XS
SM
MD
LG