Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilan Amurka, Canada da Tarayyar Turai sun fice daga bikin rantsar da shugaban Uganda


Shugaban Uganda Yoweri Museveni
Shugaban Uganda Yoweri Museveni

Jiya Alhamis yayinda ake bikin rantsar da shugaban Uganda Yoweri Museveni wakilan kasashen Amurka, Canada da na yammacin turai suka fice saboda kasancewar shugaban Sudan da kotun kasa da kasa ko ICC take tuhuma tuhuma da kuma kalamun shugaban Ugandan inda ya caccaki kotun

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka tace wakilan Amurka sun fice daga bikin saboda kasancewar Shugaban Sudan Omar al-Bashir wanda kotun kasa da kasa na manyan laifuka dake Hague ta tuhuma da laifin kisan kare dangi da ya yi a yankin Dafur cikin Sudan din.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka tace Amurka ta damu cewa Shugaba Bashir ya iya balaguro zuwa Uganda, kasar da take cikin kotun kasa da kasa ko ICC. Kasancewa tana cikin kotun kamata ya yi ta tsareshi ta kuma mikashi ga kotun. Ba shi kadai ba duk wanda kotun ke zarga da wani laifi idan har ya shigo kasarta yakamata ta mikashi ga kotun ne. Maimakon hakan Museveni a jawabinsa jiya Alhamis ya fito fili ya nuna wa kotun bakin raini.

Da yake yiwa shugabannin Afirka jawabi, Museveni yace shi yanzu ya dawo daga rakiyar kotun domin cike take da mutanen banza mutanen wofi marasa imani. Da ya yi wadannan kalamun ne wakilan Amurka da Canada da na tarayyar turai suka fice.

Wannan wa'adin mulki shi ne na biyar da za'a rantsar da shugaban wanda ya kama madafin ikon kasar a shekarar 1986.

Magoya bayan Shugaba Yoweri Museveni sanye da riguna masu launin tutar jam'iyyar shugban
Magoya bayan Shugaba Yoweri Museveni sanye da riguna masu launin tutar jam'iyyar shugban

XS
SM
MD
LG