Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Kasar Liberia Ya Shiga Amurka da Cutar Ebola


Asibitin da aka kwantar da wanda yake dauke da cutar ebola a Dallas jihar Texas.
Asibitin da aka kwantar da wanda yake dauke da cutar ebola a Dallas jihar Texas.

A Karon farko an samu bullar cutar ebola a kasar Amurka da wani dan kasar Liberia ya shigo da ita.

Jami’an kiwon lafiya na jihar Texas a nan Amurka suna sa ido akan wasu mutane 80 ko sun kamu da cutar ebola. Cikin mutanen 18 sun yi cudanya da mutumin Liberian da ya zama na farko da aka sameshi da cutar ebola a Amurka.

Mai Magana da yawun hukumar kiwon lafiya Erikka Neroes ta karamar hukumar Dallas tace kawo yanzu babu daya daga cikin wadanda suke sama ido da ya nuna alamar kamuwa da cutar.

As samu Duncan wanda ya fito daga Liberia da cutar ebola ranar Lahadi. Yana ware a wani asibiti a Dallas inda aka ce yana cikin wani hali mai tsanani.

Jiya Alhamis a Landan Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya Philip Hammond yayi gargadi a dauki mataki kai tsaye domin a yaki barkewar Ebola, cutar da tuni ta kashe mutane fiye da 3,300 a Yammacin Afirka.

A wani taro akan kwayar cutar yace daukan matakai kai tsaye zai kare rayukan dubun dubatan mutane ya kuma hana cutar zama annoba ta gama gari.

Kasashen Birtaniya da Saliyo sun shirya taron ne domin su wayar da kawunan jama’a akan yadda cutar ta yadu lamarin da yasa suka nemi goyon bayan kasashen duniya tun kafin a yi taron masu bada doki da aka shirya nan gaba a wannan watan.

Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ko WHO a takaice,tace kwayar cutar ebola ta kama mutane fiye da 7,100 wadanda yawancinsu suna kasashen Saliyo da Guinea da Liberiya ne.

XS
SM
MD
LG