Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Jirgi Mai Saukar Ungulu Ya Fadi a Adamawa


Wani jirgi mai saukar ungulu ya fadi a hedikwatar jihar Adamawa, turawa biyar ne dai turawa ke cikin jirgin.

Haka kuma rahotanni sun kara da cewa akwai yiwuwar jirgin na leken asiri ne, domin bai yi kama da jiragen da ake kai hare-hare da su a yankin ba.

Jami'an sojin Najeriya dai daga bisani sun killace wurin da jirgin ya fadi kuma sun hana 'yan jarida kaiwa inda ya ke.

Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa da ta fito daga hukumomin Nigeria game da faduwar jirgin.

XS
SM
MD
LG