Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Jirgin Saman 'Yan Sama Jannati Na Kasar Rasha Ya Tarwatse


Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin

Wani jirgin 'yan sama jannati na kasar Rasha wanda bashi da matuki, ya tarwatse a sararin samaniyar Saberiya jiya Alhamis minti shida bayan da ya tashi daga kasar kazakhstan.

Hukumar binciken sararrin samaniya na Rasha yace jirgin ya tarwatse ne bayan yayi tafiyar kilomita 190 daga doron kasa.

Galibin baraguzan jirgin da kayayyaki da ya dauka sun kone a sararin samaniya. Sauran abunda ya rage bai kone ba ya fadi a wani wuri mai nisa a kasar Saberiya ba nisa daga kan iyakar kasar da Mongolia. Babu rahotannin cewa tarwatsewar ta jikkata mutane ko ta haddasa wata barna ba. Ana ci gaba da binciken musabbabin tarwatsewar jirgin.

XS
SM
MD
LG