Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Jamus Ta Kada Kuri'a Akan Kisan Armeniyawa da Turkiyya Ta Yi


Turkiyya ta amsa kashe dubban Armeniyawa amma ta ki yadda cewa wani yinkuri ne na karar da wani jinsi

'Yan Majalisar Dokokin Jamus sun kada kuri'a yau Alhamis, ta amicewa da kisan Armeniyawan da Turkiyya ta Daular Usmaniyya ta yi, yayin yakin duniya na 1 a matsayin kisan kare dange.

Tunda farko Shugaban Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ya yi gargadin cewa muddun aka amince da kudurin a matsayin doka, dangantakar kasashen Turkiyya da Jamus ta fuskar diflomasiyya da tattalin arziki da cinakayya da siyasa da soji za ta yi tsami.

Armaniya ta ce an kashe mutane miliyan 1 da rabi tsakanin 1915 da 1917. Turkiyya ta amsa cewa an kashe dubban Armeniyawa, to amma ta ki yadda cewa wannan kisan wani yinkuri ne na karar da wani jinsi.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG