Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wannan Harin Ta'addanci Ne - Sweden


Jami'an asibiti da na 'yan sanda a yankin da aka kai hari da babbar mota a birnin Stockholm na Sweden
Jami'an asibiti da na 'yan sanda a yankin da aka kai hari da babbar mota a birnin Stockholm na Sweden

Hukumomi Sweden sun ce harin da aka kai a birnin Stockholm, hari ne na ta'addanci yayin da jami'an tsaro suka fara neman wani mutum da ake zargi na da hanu a harin.

Akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu bayan da wani direban babbar mota ya bi ta kan masu tafiya a gefen hanya a birnin na Stockholm.

'Yan sandan birnin sun tabbatar cewa rayuka sun salwanta tare da wasu da suka jikkata da dama ba tare da sun bayyana ainihim adadin mutanen ba.

Sun kuma kara da cewa babu wanda aka kama da laifin wannan aika-aika, amma dai sun ce suna yi wa wasu mutane biyu tambayoyi.

Firai ministan Sweden Stefan Lofven ya kwatanta harin a matsayin na ta'addanci.

"Gwamnati na iya bakin kokarinta domin ganin ta gane mai ya faru." In ji Lofven.

Hakan na faruwa ne yayin da jami'an tsaro suka bayyana cewa suna neman wani mutum da ake ganin zai iya taimaka wa wajen ba da bayanai kan lamarin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG