Sakataren ma’aikatar tsaron cikin gida na Amurka John Kelly da sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka Rex Tillerson sun gana da shugaban kasar Mexico Entique Pena Nieto da ministocin kasar da suka bayyana damuwa da rashin jin dadin matsayin Trump a kan huldar shige da fice da kuma cinikayya da Mexico.
Kelly ya jadada cewa, ba za a dauki matakin soji wajen kama bakin haure karkashin shirin shugaba Trump na tasa keyar bakin haure dake Amurka ba.
Tillerson ya fada a wata sanarwa cewa, an yi tattaunawa mai ma’ana.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka bata yi wani Karin haske dangane da tattaunawar da aka yi da shugaba Pena Nieto ba.
Facebook Forum