Accessibility links

Wasu Matasan Arewa Sun Ce Janar Buhari Ya Hakura

  • Halima Djimrao

Janar Muhammadu Buhari.

Janar Muhammadu Buhari.

Kungiyar "Arewa Youth Development Foundation" ta yarda da matsayin Dakta Ahmed Gumi akan takarar Janar Buhari a shekarar 2015.

Wata kungiyar matasan arewacin Najeriya mai suna “Arewa Youth Development Foundation” da turancin Ingilishi, ta ce akwai bukatar ‘yan arewa su sake yin nazari su yi karatun ta natsu game da maganar da Dakta Ahmed Gumi yayi akan takarar Janar Muhammadu Buhari a zaben shekarar 2015.

Mallam Yahaya Kanem shi ne shugaban wannan kungiya ta matasa, kuma ya ce, duk da yake dai dan arewa suke so a tsaida takara a zaben shugaban kasa a shekarar 2015, amma dai ya kamata janar Muhammadu Buhari ya hakura.

Wakilin Sashen Hausa a Kaduna, Isa Lawal Ikara ne ya aiko da rahoton.

XS
SM
MD
LG