Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Ministocin Najeriya Sun Tabbatar da Tabarbarewar Tattalin Arzikin Kasa


Kemi Adeosun, Ministar Kudin Najeriya
Kemi Adeosun, Ministar Kudin Najeriya

Ministan kudin Najeriya Mrs. Kemi Adeosun da Ministan kasafin kudi da tsare tsare Udoma Udo Udoma a lokuta daban daban sun ce tattalin arzikin kasar na cikin wani mawuyacin hali

Duk da amincewarsu sun ce yanayin kunci da ake ciki ba zai dore ba domin za'a shawo kanshi.

Wani Malam Ahmed Yusuf tsohon babban darakta a bankin Unity yace an shiga wannan mawuyacin halin ne domin gwamnatocin baya basu yi wani tanadi ba dangane da kudaden shiga da aka dinga samu a can baya.

Dalili na biyu shi ne faduwar darajar mai da farashinsa a kasuwannin duniya. Idan farashinsa bai sake tasowa ba haka lamarin zai cigaba.

Yace a tsarin da gwamnatin Buhari ta fito dashi dole ne mutanen kasar su fara shuka abun da suke ci. Kayan masarufin da kasar ke anfani dasu su kasance abun da 'yan kasa suka shuka ne suka sarafa ba wai an shigo dasu daga waje ba.

Ta hanyar noma gwamnati ta fara aiki yadda ya kamata fata nan shi ne noman ya dore amma dole a jira lokacin da za'a fara samun albarkatun noma.

Na biyu a samo kudin shiga koda ma bashi za'a ci a baza cikin jama'a za'a samu masalaha musamman idan an yi anfani dashi ta hanyar da ta kamata domin gujewa wata matasalar kuma.

Abu na uku a jawo jihohi su tsaya tsayin daka su kula da tattalin arziki domin a samu fita da wuri.

Dr Obadiah Mailafiya tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya yace rashin samun kwararru dake ba shugaban kasa shawara akan tattalin arziki ya sa aka shiga mawuyacin hali kamar wannan. Gwamnati bata da kungiyar masana tattalin arziki da take aiki dasu.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:39 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG