Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Sandan Najeriya Ya Fasa Kwai - Kashi na Biyu


A cigaba da firarsu dansandan Mopol din nan ya nuna cewa mugun kuskure ne mutum ya kai kuka akan rashin adalcin shugabanninsu da zaluncin da su keyi gaban hukumarsu domin za'a azaftar da mutum a ce ya tonawa manyansa asiri.

Yayin da shugabanninsu na can koli ke zaluntarsu wasu na tsakiya suna jin tausayi kuma su kan fitar da kudin kansu su basu domin su ci abinci. Suma suna bakin cikin irin ukubar da suke sha a dajin Borno. Yace babu abun da ba zasu iya yi ba amma wa zai fito da aminci da adalci. Duk cikin shugabanninsu wanene zai fito ya nuna bakin ciki akan abubuwan dake faruwa a kasar. Kananan yansanda a jihar Borno babu inda zasu kai kukansu yau. Yace suna cikin wahala. Sun yi kuka har ya ishesu. Sai dai Allah Ya dauki fansa.

Shugabannin arewa basu taso su taimaki jama'arsu ba. An bar mutane kara zube. Dole su shiga wata hanya da bata kan kaida. Arewa tana lalacewa kuma ita ma kasar zata bi sawu. An dauko sojojin kasashen waje su yi yaki a Najeriya. Amma ga kayan aiki sun ki su na gida su yi aiki. Shin wai ana son su kama 'yan ta'adan ne da hannayensu. Idan ba'a basu kayan aiki ba babu abun da zasu iya yi. Yace idan aka shiga barikin 'yansandan jihar Borno za'a tarar da kayan aiki a zube amma wanene zai bayar da su a yi aiki. Sai dai a jira mutane su mutu kana a gayawa gwamna ana bukatar kaza. Idan an karba kuma ba za'a bayar ba.

A firar da gwamnan yayi yace duk wani jami'in tsaro da ya rasa ransa akan ba iyalansa nera miliyan guda. Shi Mopol yace gaskiya ne gwamnan yana bayar wa kuma yana sa ido ya tabbatar kudin ya kai wurin iyalan. Yace gwamnan yana kokari.

Mopol ya jaddada cewa a basu kayan aiki a ga abun da zai faru. Allah muke bautawa zai yi taimako. Yace wahalar da suke ciki Allah ne Ya barsu cikinta domin rashin gaskiyar shugabanninsu.

Akan dalilin da yasa ba za'a basu kayan aiki ba sai Mopol yace ba zasu bayar ba domin shugabanninsu suna son su je yaki ba kayan aiki su mutu domin a ci dukiya a kansu. Hatta kayan jiki na sawa da aka kawo shugabanninsu sun hana na kasan. Wadanda suke aiki cikin ofis aka ba amma wadanda ke bakin daga ba za'a basu ba. Daga baya kuma an nuna a telibijan cewa an ba kowa rigunan aiki.

Bayan jin wannan ne, Sashen Hausa na Muryar Amurka ya tuntubi tsohon Sfeto Janar na 'yan Sandan Najeriya Muhammadu Gambo Jumeta, wanda yace wannan lamari na ta'addanci bakon abu ne ga 'yan sanda.

JUMETA: Tun ma basu fara magana ba, mu mun gani. Munyi nazarin abubuwan da yawa kullum, mun gani cewa ba yau ba, an dade, wato suna cikin wani hali wanda yake, babu wanda ke ji musu cewa ko sauraron koke-kokensu, sun kansu ‘yan sanda da kuma soja. Tunda kuma aka fara abunnan, wadannan koke-koken, suna nan ana ta yinsu, amma wato a samu a magantasu, babu saurin da ake bukata.


Wannan shine kashi na biyu na hira da Muryar Amurka yayi da dan sanda. A kwanaki masu zuwa, zamu kawo ragowar hirar.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG