Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Sun Fito da Hanyar Magance Satar Shanu


Shanu
Shanu

Yawan sace sacen shanu a wasu sassan Najeriya sun sa wasu kwararru sun fito da wata hikima ta yadda za'a gane kowace saniya da wanda ya mallaketa da kuma sanin shin ya sayar ne ko kuwa saceta aka yi.

Tsarin tsamo shanun da ake sacewa a Najeriya wanda wasu kwararru da hadin kan wani kamfanin sadarwa a Najeriya na nufin ganin koda an sace saniya to ba zata yiwu a sayar da ita ba saboda akwai yadda za'a gano mai ita.

Alhaji Ibrahim Maigari Ahmadu shi ne shugaban kamfanin kwararrun da suka fito da sabuwar hikima tare da hadin gwuiwar wani kamfanin sadarwa.

A taron jihohin arewa 19 na masu ruwa da tsaki da aka gudanar a garin Kaduna Alhaji Ahmadu ya yiwa manema labaru karin haske dangane da shirin.

Yace sama da shekaru biyu ko ukku suka dinga tunanen yadda zasu sami hanya mafi sauki su magance matsalar sace-sacen shanu. 'Yar naurar da ake sawa jikin dabbar zata nuna lamabar mai ita.

Alhaji Lawal Batagarawa ya bada jawabin wayarda kawunan Fulani akan yadda za'a dakatar da sace sacen shanu a Najeriya kuma ya gargedsu da su rungumi sabon shirin.

Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG