Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Yan Jihar Inugu Na Son Fulani Makiyaya Su Bar Musu Yanki


Rikicin dake ci gaba da afkuwa tsakanin Fulani Makiyaya da Masu Gonaki musamman a Kudu maso Gabashin Najeriya, na ci gaba da daukar hankula sanadiyar samun salwantar rayuka da akeyi.

Rigimar baya bayan nan itace wadda ta faru a jihar Inugu, inda aka samu asarar rayuka masu yawa, hakan yasa gwamnonin yankin biyar da sarakunan gargajiya gudanar da tarurruka. Sai gashi wasu al’umomin jihar sun bayyana matsayinsu na cewar basa bukatar Fulani makiyaya su ci gaba da karakaina a yankin.

Wani daga cikin mazauna yankin na cewane yawancin lokuta Fulani na bin ta kauyukansu rike da bindigogi da sauran makamai, haka kuma suna cin zarafin matansu, don haka basa bukatar sasantawa abinda suke so shine Fulani su bar musu yanki.

Dayawa daga cikin yankin dai na nuna rashin goyon bayansu ga hukuncin da aka yanke na yiwa Shanun Fulani hanyarsu ta musammam.

Saurari cikakken rahotan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG