Wata babbar fashewar da ake kyautata cewa bom ne, ta afkawa ofishin ‘yan sanda a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bada rahoton cewa Fashewar tayi raga-raga da kofar shiga harabar ofishin ‘yan sandan.
Shaidun gani da ido suka ce an rasa rayuka, mafi yawansu kuma ‘yan sanda ne.
An aza laifin kai harin a kan ‘yan kungiyar Boko haram, kungiyar da ta maida Borno tamkar sansaninta a Nigeria.