Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kotun Amurka Ta Yiwa Dan Kungiyar al-Qaida Daurin Shekaru 40


Shugaban al-Qaida Osama bin Laden da Amurka ta ga bayansa
Shugaban al-Qaida Osama bin Laden da Amurka ta ga bayansa

Wata kotu a nan Amurka ta yiwa wani dan asalin kasar Pakistan daurin shekaru arba'in saboda an sameshi da laifin shirya kai harin bam a wani katafaren shagon kasuwanci na Birtaniya da New York.

Tun farkon wannan shekarar kotu ta samu Abid Naseer dan shekarau 29 da haihuwa da laifin samar ma kungiyar al-Qaida goyon baya tare da tanada mata wasu kayan aikata ta'adanci da nufin haddasa muguwar barna.

Jiya Talata Mai shari'a Alkali Raymond Dearie na kotun gwamnatin tarayyar Amurka dake Brooklyn ya gayawa Naseer yace "Kai ba ma'aikata laifi ba ne kawai.Kai dan ta'ada ne"

An fara kama Naseer a Birtaniya ne a shekarar 2009 inda ya jagoranci wani bangaren al-Qaida dake kokarin kai hari a wurin kasuwanci a Manchester. Harin yana cikin jerin hare-haren da suka shirya da suka hada da jefa bama bamai a layin dogon karkashin kasa na birnin New York tare da kai hari kan ofishin wata jaridar kasar Denmark.

Kodayake ba'a tuhumeshi a Birtaniya ba amma an tasa keyarsa zuwa Amurka a shekarar 2013 domin ya fuskanci shari'a akan kokarin kai hari a New York.

Tun farko wasu mutane biyu Najibullah Zazi da Zarein Ahmedzay sun amsa laifi a wani kotun gwamnatin tarayyar Amurka dangane da kokarin kai hari New York.

Naseer wanda ya kare kansa da kansa a shari'ar ya girma Peshawar ne cikin kasar Pakistan. Yace shi mai buga kwallon gora ne. Ya kuma sha alwashin daukaka kara

XS
SM
MD
LG