Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kungiyar Agaji Ta Dauki Ma’aikatan Polio 350 A Jihar Bauchi


Kungiyar mai suna Volunteer Community Mobilisers ta ce ta dauki ma’aikatan ne a kananan hukumomin Bauchi da Toro domin bunkasa aikin rigakafin Polio a yankunan

Wata kungiyar agaji mai suna Volunteer Community Mobilisers, ko VCM a takaice, ta dauki ma’aikata ‘yan agaji su 350 a jihar Bauchi domin bunkasa ayyukan rigakafin Polio a Jihar.

Shugaban kungiyar, Alhaji Auta Kawu, ya fada lahadin nan a Bauchi cewa sun dauki wadannan ‘yan agaji ne a yankunan kananan hukumomin Bauchi da Toro, kuma a yanzu haka sun a cikin masu aikinrigakafi a wadannan yankuna biyu.

Ya kara da cewa wadannan ‘yan agajin suna kuma ilmantar da jama’a kan muhimmancin awun ciki ga mata masu juna, da kuma sauran alluran rigakafin da ake ba yara.

Yace irin matakan da kungiyarsa tare da wasu hukumomin suka dauka sun kai ga taimakawa wajen rage yaduwar cutar shan inna ta Polio, wadda aka samu yara biyar da suka kamu da ita a shekarar 2013, amma a watanni uku na farkon wannan shekara ba a samu ko guda daya ba.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG