Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata 'yar Najeriya ta taka rawar gani a fannin ilimi a Amurka


Dalibai dake yawan zanga zanga a Najeriya
Dalibai dake yawan zanga zanga a Najeriya

Shekaru biyu a jere, matasa daga Nijeriya na cimma wani babban burin da daliban makarantar sakandare kalilan ke cimma—watau samun a dauke su a dukan manyan jami'o'in Amurka da a ake kira Ivy League.

An ba Agusta Uwanmanzu-Nna, wadda ‘iyayenta suka kaura zuwa Amurka daga Najeriya, daga nan zuwa daya ga watan Mayu ta zabi makarantar da take so ta tafi daga cikin fitattun jami’oin Amurkan.

Bara wani dalibi haifaffen Najeriya Harold Ekeh ya zabi zuwa jami’ar Yale bayanda aka dauke shi a duka fitattun jami’oin takwas.

Duka dabilban biyu sun yi karatu ne a makarantar sakandare ta Elmon Memorial dake New York.

An kuma dauki Uwamanzu-Nna a wadansu karin jami’oi hudu da ta nemi shiga da suka hada da Jami’ar John Hopkins, Jami’ar fasaha ta Massachusetts, jami’ar New York ko NYU da kuma makarantar fasaha ta Resselaer.

Uwamanzu-Nna ta shaidawa wata tashar talabijin cewa, “ko da yake an haifeni a nan Amurka, na ziyarci Najeriya a lokuta da dama. Na kuma ga ‘yan’uwana da basu da irin wannan damar da na samu. Saboda haka, dukan abinda nayi, zan tabbata ya daga mutumcin Najeriya.”

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG