Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wayar Da Kan Al'umma Kan Tazarar Haihuwa


Wadansu mata suna kallo a dakin jinya
Wadansu mata suna kallo a dakin jinya

Kungiyar WRAPA ta yaba yadda kungiyoyi da malamai suka tashi tsaye haikan wajen wayar da kan al’umma a kan muhimmancin tazarar haihuwa

Kungiyar WRAPA mai fafatukar nemarwa mata hakinsu ta yaba yadda kungiyoyi da malamai suka tashi tsaye haikan wajen wayar da kan al’umma a kan muhimmancin tazarar haihuwa wadanda idan aka kiyaye zai rage mace-macen mata yayin haihuwa.

A cikin hirarsu da wakilin sashen Hausa Nasiru Yakubu Birnin Yero, mallam Abbas Shehu jami’in tsare-tsaren kungiyar WRAPA a Kaduna, yace abinda yafi damunsu ba kawai abinda ya shafi tazarar haihuwa bane, amma abinda yafi damunsu shine abinda yake faruwa a wadansu lokuta inda ake tarar da mata a gidajensu ainda abubuwan da ya kamata a kula da su da ya shafi daukar ciki da kulawa da ita matar lokacinda ta dauki ciki da lokacin da zata haihu, da abinda take bukata bayan ta haihu da kuma shi kansa yaron, sai kaga mafi yawanci ba a kulawa da shi duk da yake addini ya bada damar kulawa da mata da abinda aka Haifa.

Mallam Shehu Abbas ya bayyana cewa haihuwa a gida yana da hadari domin idan aka sami matsala, yana da wuya a iya taimakonta idan ba a kaita asibiti ta sami kulawa cikin sauri yadda ya kamata ba.

Samun tazatar haihuwa tsakanin haihuwa na daga cikin abinda masana suka bayyana a matsayin daya daga cikin abinda ke sa mata koshin lafiya da kuma kaucewa mace-macen matan yayin daukar ciki da haihuwa.

Hira Da Shehu Abbas Kan Tazarar Haihuwa - 1:30
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
Shiga Kai Tsaye

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG