Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Dace a Kara wa Maaikata Albashi, Domin Rage Cin Hanci da Rashawa


ABUJA: Ranar Ma'aikata
ABUJA: Ranar Ma'aikata

A bukuwar ranar maaikata da aka gudanar a duk fadin duniya, batun da yafi daukar hankali a Najeriya shine na Karin albashi.

Kusan duk wanda wakilin sashen Hausa Babangida Jibrin yay Magana dau shine albashin dubu #18 mafi karanci yayo kadan.

Ga ma abinda wani maaikacin gwamnatin ke cewa.

Ya kamata gwamnati ta duba wannan al’amari, domin irin hakan shi zai taimakawa yaki da ake yi da cin hanci da rashawa, saboda idan ka koshi ina ruwa ka da wani cin hanci da rashawa.

Amma kana karban #18,000 Mallam kaga an kawo maka harka data kunshi dubban Nairori ko miliyoyi, ka iya kauda kai?

#18,000 ne gwamnati tarayya da wasu jihohin Najeriya ke biya a matsayin albashi mafi karanci banda gwamnatin jihar Zamfara kamar yadda rahotanni ke cewa.

A karshen bikin ranar maaikata da aka gudanar, Maaikatan su bukaci gwamnatin tarayya data biya albashi mafi karanci na #56,000.

Kungiyar kwadagon ta Najeriya tace ta yanke wannan adadin ne ta la’akari da halin matsin tattalin arziki da kasar take fuskanta.

Ga Babangida Jibrin da cigaban Rahoton 2’50

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG