Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Zaka Iya Karre Kanka Daga Hawan Jini


Ana gwajin hawan jini
Ana gwajin hawan jini

Hawan jinni ya fara zama wata babbar kalubala ga lafiya. Hawan jinni wani yanayi ne inda karfin bugun jinni a cikin jijioyin jinni yake hawa fiye da yada ya kamata.

Hawan jinni ya fara zama wata babbar kalubala ga lafiya. Hawan jinni wani yanayi ne inda karfin bugun jinni a cikin jijioyin jinni yake hawa fiye da yada ya kamata.

Idan mutum ya kamu da hawan jinni, babu wani takamammen magani. Mutum zai ci gaba da shan magani har iya tsawon ransa kuma yana iya kamuwa da wadansu matsaloli sakamakon magungunan da yake sha.

Idan ba’a yi maganin hawan jinni ba, zai iya haifas da matsaloli da yawa kamar su makamta, lalacewar koda, ciwon zuciya, da dai saurans. Abu mafi kyau shine a yi kokari a kare kai daga kamuwa da hawan jinni. Akwai wadansu yanayi da zasu iya zama da wuya a kiyaye kamar su tsufa da kuma gado.

Amma dukan sauran abubuwan da ke kawo hawan jinni za’a iya karesu. Shan giya wata babbar kafa ce ta kama hawan jinni. Gujewa shan giya zai iya kare hawan jinni har ma da wadansu matsaloli na lafiya.

Wani abu dake da muhimmanci idan ana maganar hawan jinni shine irin abincin da mutum ke ci. Abincin dake kunshe da gishiri da kuma kitse mai yawa yakan iya kawo hawan jinni. Abincin da aka gyara aka sa a gwangwani yana iya kawo hawan jinni domin yana cike da gishiri. Abincin da ake toyawa kamar su burodi, madara da kayan da aka yi da nono suna cike da kitse da kuma gishiri. Guje masu da kuma cin kayana lambu da yayan itatuwa da kuma hatsin da ba’a cire bayan ba yana taimakawa.

Motsa jiki na taimakon kone yawan kitse da kuma kare hawan jini. Kimanin motsa jiki na minti 30 kowace rana yana da amfani. Idan ba’a iya yi kowacce rana ba, to a yi sau uku a sati. Yin tafiya a kafa da sauri, iyo a ruwa, gudu a hankali (sassafa) da yoga, na da mahimmanci domin karewa da kiyaye hawan jini.

Idan aka dade ana shan wadansu magunguna kamarsu corticosteroids, kwayoyin hana daukar ciki na hadiya, na iya kawo hawan jini. Don haka sai a sha wannan a yayinda ya kamata kuma na dan lokaci.

Matsuwa ta jiki da ta kwakwalwa ma na iya kawo cutar ciwon zuciya.

Kada kayi abubuwa fiye da kima. Cin abinci mai kyau zai iya taimakon irin Karfi da kuma iyawarka. Kiyaye gajiyar kwakwalwa yana iya zama kariya ta hawan jini. Yoga na taimakawa wajen hutar da jiki da kuma kwakwalwa.

Koda mutum ya kamu da hawan jini, wadannan hanyoyi zasu taimaka wajen rage muninsa ba tare da shan magunguna masu yaw aba.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG